An sake sassauta dokar hana zirga-zirgar babura masu kafa uku a wasu sassan jihar Adamawa

0 245

Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya sake sassauta dokar hana zirga-zirgar babura masu kafa uku da aka fi sani da Keke Napep a kananan hukumomin Yola ta Arewa, Yola ta Kudu da kuma Girei.

Gwamnan, a cikin wata sanarwa a jiya ta hannun babban sakataren yada labaran sa Mista Humwashi Wonosikou, ya ce dokar wacce a baya take daga karfe 10 na dare zuwa 5 na safe, an sauƙaƙa ta 11 na dare zuwa 5 na safe kullum.

A watan Fabrairun 2021 ne gwamnatin jihar ta sanya dokar hana zirga-zirgar ababen hawa a kananan hukumomi uku ta jihar Adamawa. Fintiri, ya yi kira ga mazauna yankin da kada su yi duk wani abu da zai iya mayar da hannun agogo baya dangane da nasarar da aka samu na samar da zaman lafiya a jihar, amma a ci gaba da rayuwa cikin aminci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: