An rufe wani wurin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a Abuja

0 201

Gwamnatin tarayya ta rufe wani wurin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a yankin Gaube, dake karamar hukumar Kuje a babban birnin tarayya Abuja, inda ta cafke wasu mutane uku da ake zargi da hannu a yunkurin da take yi na yaki da hako ma’adinai ba bisa ka’ida ba da kuma asarar kudaden shiga a bangaren ma’adanai.

Sanarwar da ma’aikatar bunkasa ma’adanai ta kasa ta fitar ta ce, an gudanar da samamen ne karkashin jagorancin John Onoja Attah, ta hanyar tattara bayanan sirri.

An bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa wadanda ake zargin ba su da wasu takardu da suka basu izinin aikin hakar ma’adinai a wurin.

Sanarwar ta kara da cewa, wani halaltaccen kamfanin hakar ma’adinai da ke da izinin hakar  ma’adinai a gurin bai samu damar shiga wurin ba saboda ayyukan masu hakar ba bisa ka’ida ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: