Jami’an kasar Kenya sun harba hayaki mai sa hawaye kan masu zanga-zangar a yau laraba yayin da suka bijirewa dokar hana ‘yan sanda shiga zanga-zangar da madugun ‘yan adawa Raila Odinga ya kira kan amincewa da karin haraji.
An rufe shaguna, an kuma tsaurara matakan tsaro a babban birnin kasar Nairobi, inda ‘yan sanda suka baza hayaki mai sa hawaye kan masu zanga-zangar da suka yi jifa da duwatsu a unguwar marasa galihu na Mathare.
An kuma yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa jama’a a birnin Mombasa mai tashar jiragen ruwa.
Zanga-zangar da aka gudanar a makon da ya gabata a wasu garuruwa da dama ta rikide zuwa tarzoma, inda aka kashe mutane shida a cewar ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar. Ko a ranar juma’ar data gabata ma sai da ‘Yan sanda suka harba hayaki mai sa hawaye a Nairobi, inda suka nufi ayarin Odinga, kuma sun dauki irin wannan matakin na adawa da zanga-zangar a biranen Mombasa da Kisumu.