An Rantsar Da Sabon Kwamishinan Yaɗa Labarai A Jigawa

0 368

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya rantsar da Alhaji Bala Ibrahim Mamser a matsayin sabon kwamishinan yada labarai matasa , wasanni da kuma aladu.

A jawabinsa bayan kammala rantsuwar, Gwamna Badaru Abubakar ya bayyana Alhaji Bala Ibrahim a matsayin haziki kuma jajirtaccen mutum wanda ya bada gagarumar gudunmawa wajen cigaban wannan gwamnati a zangon farko na gwamnatinsa.

Yayin Rantsuwar kama aiki

Yace an sake nada Alhaji Bala Ibrahim a matsayin kwamishina ne bisa cancanta inda kuma ya bukace shi da ya kara rubanya kokarinsa wajen yayata manufofin wannan gwamnati.

A nasa jawabin Alhaji Bala Ibrahim ya godewa gwamna Badaru Abubakar da gwamnatin jiha data sake bashi wannan dama.Kwamishinan sharia Dr Musa Adamu Aliyu ya rantsar da sabon kwamishinan a lokacin taron majalissar zartarwa ta jiha da aka gudanar a gidan gwamnati.

Leave a Reply

%d bloggers like this: