An raba sama da miliyan dari ga masu karamin karfi a karamar hukumar Auyo

0 304

Sama da naira miliyan dari da hamsin aka raba ga masu karamin karfi a karamar hukumar Auyo karkashin shirin gwamnatin tarayya na tallafawa masu karamin karfi.

Da yake jawabi lokacin rabon, jami’in fadakarwa na shirin a jihar Jigawa, Malam Mustapha Madobi ya ce shirin yana karkashin ma’aikatar jin kai da da walwalar jama’a an kirkiro shi ne a shekara ta 20218 domin rage talauci a tsakanin al’umma.

Malam Mustapha Madobi ya ce sama da mutane dubu dari da saba’in ne suka samu nasarar shiga cikin shirin a jihar Jigawa.

Shima a jawabin sa shugaban karamar hukumar Auyo Alhaji Muhammad Ahmad Sani ya yabawa gwamnatin tarayya da ta jihar jigawa wajen kirkiro da shirin domin bunkasa tattalin arzikin al’umma.

Ya yi kira ga masu amfana da shirin da su yi kyakkyawan amfani da tallafin wajen inganta rayuwar su tare da cigaba da yiwa shugaban kasa Muhammad Buhari da gwamna Muhammad Badaru Abubakar addua a musamman kan ingantuwar al’amuran tsaro da bunkasar tattalin arziki.

Da yake jawabi Jagoran tawagar masu aikin biyan tallafin a jihar jigawa, Mista Samuel Ojerinde ya ce ana gudanar da biyan ne ta na’urar zamani domin kaucewa samun matsala.

Ya taya masu amfana da shirin murna tare da yabawa masu gudanar da biyan tallafin kan kokarin su na gudanar da biyan cikin gaskiya da adalci.

Kowanne daga cikin masu amfana da shirin ya karbi naira dubu ashirin a matsayin ariya na watanni hudu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: