An Raba Kuɗi sama da Naira Miliyan 94 ga Matasa Marasa Aiki A Jigawa

1 324

Jagoran shirin aikin gona na Fadama kashi na 3, a jihar Jigawa, Alhaji Aminu Isah, yace shirin ya raba Naira Miliyan 94 da Dubu 400, ga matasa marasa aikin yi, su 253, a jiharnan, domin fara sana’ar noma.

Aminu Isah, na magana ne yayin taron karawa juna sani, da aka gudanar a Birnin Dutse, jiya Asabar, akan bukatar yin amfani da kudaden ta hanyar data dace, domin cimma bukatar shirin.

Yace matasan, da suka hada da mata da maza, an zabo su ne daga Kananan Hukumomi 27 na Jihar.

Jagoran yace wadanda suka amfana, sun samu horo akan sarrafa shinkafa, da kiwon kaji, da kiwon kifi, da sauran harkokin kasuwancin noma.

Aminu Isha, yace hakan na daga cikin shirin gwamnatin tarayya wajen samar da ayyukan yi ga dumbin matasa.

Yace banda wannan kuma, gwamnatin jihar Jigawa, na taimakawa kimanin matasa 300, akan sana’ar aikin gona.

Jagoran sai ya bukaci wadanda suka amfana, da su tsara shirin kasuwancinsu, kuma su karance shi sosai, kafin su aiwatar.

  1. Sani kainuwa says

    To ba’ace komai ba dangane da tallafin jigawa ga matasa

    Daga sani Kainuwa

Leave a Reply

%d bloggers like this: