Mai martaba Sarkin Kazaure Alhaji Najib Hussaini Adamu ya nada sabbin Yaran Sarki guda goma 18.
Wadanda aka nada sun hadar da Tasi’u Shehu Sa’idu Wazirin Shamaki da Shamsiddin Sani Shehu Galadiman Shamaki da Mudassiru Lawan Yariman Shamaki da Alhaji Sani Idris Galadiman Sarkin Bai da Babandi Ibrahim Wazirin Sarkin Makera.
Sauran sun hadar da Salisu Isya Wazirin Sarkin Yaki da Dahiru Lawan Wakilin Sallama da Bashir Yusuf Wazirin Sallama da Bello Abdulkadir Sarkin Gida da Muftahu Abdul Matsayin kuraye da Bashir Gudaji Kaigama da Lawan Danfaranshi Bargai da kuma Alhaji Murtala Muhammad Sarkin Hatsi.
A Jawabinsa Jim kadan bayan nadin, Mai martaba Sarkin Kazaure Alhaji Najib Hussaini Adamu ya hori sabbin Yaran Sarkin dasu zama Masu kokari da Jajircewa dan ciyar da Masarautar gaba.
Mai martaba Sarki ya kuma yi kira ga sabbin Yaran Sarkin dasu zama Masu biyayya da Da-a da bin nagaba domin sanin Al amuran aiyukan Mulki.
Sarkin ya yi musu Addu’ar fatan Alkhairi.