An nada Nilfa Gambo ‘yar shekara 34 a matsayin alkalin babbar kotun jihar jigawa

0 234

A jiya ne Gwamna Umar Namadi ya rantsar da ‘yar shekara 34 mai suna Nilfa Gambo a matsayin alkalin babbar kotun jihar.

An rantsar da Nilfa Gambo ne a zauren majalisar da ke gidan gwamnati, tare da Muhammad Usman a matsayin alkalan babbar kotu.

Da yake jawabi bayan rantsarwar, gwamna Namadi ya ce duk nade-naden an yi su ne bisa cancanta, ya kara da cewa sabbin wadanda aka nada sun sanya jihar alfahari da yadda suka yi fice a yayin da ake tantance su.

Gwamnan ya taya sabbin alkalan murna tare da umartar su da su yi aiki da himma da tsoron Allah.

Leave a Reply

%d bloggers like this: