Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya Nema ta karɓi ‘yan ƙasar 144 da suka maƙale a Libya ranar Talata bayan isar su.
Mutanen sun sauka ne da misalin ƙarfe 5:15 na yamma a filin jirgi na Murtala Muhamed da ke Legas.
Cikin mutanen da aka kwaso akwai maza 89, mata 35, yara 17, da jarirai uku, inda ƙungiyar kula da ‘yan gudun hijira ta International Organization for Migration (IOM) ta agaza musu.
An kai su sansanin ‘yan gudun hijira na Igando bayan kammala tantance su, in ji hukumar Nema.