Jami’an ‘yan sandan China da na Afrika ta Kudu sun kwace dubban rigakafin coronavirus na bogi kamar yadda Hukumar ‘Yan Sandan Kasa da Kasa ta sanar.
Hukumar ‘Yan Sandan Kasa da Kasa ta Interpol mai shalkwaata a birnin Lyon ta ce, an gano akwatina 400 masu dauke da kwatankwacin alluran rigakafin coronavirus na bogi har guda dubu 2 da 400 da aka jibge a dakin adana kayayyaki na Germiston da ke wajen birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu.
Kazalika jami’an tsaron sun kuma gano takunkumai na bogi, sannan kuma suka kama wasu Sinawa da mutanen Zambia da aka samu cikin harkar.
A can kasar China kuwa, rundunar ‘yan sandan ta yi nasarar gano wani gungun miyagu mai sayar da alluran rogakafin Covid-19 na bogi a wani bincike da ta kaddamar wanda Hukumar Interpol ta dauki nauyi.
A samamen da ‘Yan sandan suka kai a Chinar, sun cafke mutane 80 tare da kwace rigakafin na bogi fiye da dubu 3 da aka sarrafa a wata haramtacciyar farfajiya.
Tun a farkon wannan shekarar ce, Hukumar ‘Yan sandan Kasa da Kasa ta gargadi hukumomin kasashen duniya cewa, su daura damarar tunkarar wani gungun miyagu da ke shirin samar da haramtaccen rigakafin coronavirus a zahiri da kuma yanar gizo.