An Kashe Wani Da Ake Zargin Mai Garkuwa Da Mutane Ne A Wani Artabu Da Sukayi Da Yan Sanda A Legas

0 156

Wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne a ranar Alhamis ya rasa ransa a wani artabu da suka yi da ‘yan sanda a yankin Ikorodu da ke jihar Legas.
A yayin harbe-harbe, ‘yan sandan sun kuma ceto wasu mutane biyu da masu garkuwa da mutane suka yi garkuwa da su a maboyarsu da ke yankin.
An tattaro cewa mai garkuwa da mutanen daya mutu da ‘yan kungiyarsa, a wani samame da suka yi a ranar 26 ga Maris, sun yi awon gaba da wasu mutane.
Bayan aikin, wadanda ake zargin sun tuntubi iyalan wadanda abin ya shafa kuma suka bukaci a biya su N20m domin su sako wadanda aka sace.
A yayin tattaunawa da wadanda ake zargin, an gano cewa iyalan wadanda abin ya shafa sun sanar da hukumar ‘yan sandan jihar Legas wanda suka binciko lamarin tare da kubutar da wadanda lamarin ya shafa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, a lokacin da yake mayar da martani kan lamarin, ya cewa a yayin musayar wutar da ‘yan sandan suka yi, ‘yan bingar sun harbe daya daga cikin wadanda ake zargin har lahira tare da ceto mutane biyu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: