An kashe mutum daya a jihar Jigawa a wani gangamin yakin neman zaben jam’iyyar APC a karamar hukumar Kazaure
A wani labarin na jam’iyyar APC, an kashe mutum daya a jihar Jigawa a wani gangamin yakin neman zaben jam’iyyar a karamar hukumar Kazaure.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Emmanuel Ekot, ya shaida wa manema labarai cewa, ‘yan sandan na bin sahun wanda ake zargi da kisan wanda aka ce ya gudu zuwa makwabciyar jihar Kano bayan ya aikata laifin.
Gwamnan Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ya jagoranci gangamin yakin neman zaben gwamna na jam’iyyar APC a garin Kazaure inda rikicin ya barke tsakanin kungiyoyin matasa magoya bayan jam’iyyar wanda yayi sanadiyar mutuwar mutum daya.
Mazauna garin sun bayyana sunan marigayin da Halliru Lafka mazaunin garin Kazaure.
Kisan ya haifar da zanga-zanga inda mazauna garin da suka kona allunan dan takarar Sanatan Jigawa ta Arewa maso Yamma a karkashin jam’iyyar APC, Babangida Hussaini, inda suka zarge shi da tattara ‘yan bangar siyasa, wadanda ke dagula zaman lafiyar garin.
An kasa samun Babangida Hussaini ta waya domin jin ta bakinsa kan lamarin.