An kashe mutane masu yawa galibi manoma tare da raba masu da muhallan su a jihohin kebbi da Sokoto

0 370

Yan bindiga sun kai hari a kauyuka 7 dake da iyaka da jihohin kebbi da Sokoto, inda suka kashe mutane masu yawa galibi manoma tare da raba masu da muhallan su.

Kauyukan sun hada da Zawaini, Jangargari Jaja na jihar Kebbi, da kuma kauyen Karani na jihar Sokoto.

An kogana gidaje da shaguna masu yawa yayin harin.

An rawaito cewa lamarin ya tilastawa mutane yin kaura zuwa kauyen Jarkuka dake wata karamar hukuma a Jihar Kebbi.

Gwamnan jihar Nasiru Idris ya tura da kayan agaji zuwa yankunan domin rage musu radadin abinda ya same su. Gwamnan ya tura wata tawaga karkashin kwamishinan bada agaji na jihar Muhammad Hamidu Jarkuka da kuma kwamishinan yada labarai da al’adu Yakubu Ahmed domin su kai kayan agaji yankunan da aka kai harin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: