An Kashe Mai Garkuwa Da Mutane Tare Da Ceto Mutum Biyu A Jihar Adamawa
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa tare da hadin gwiwar wasu mafarauta ta kashe wani mai garkuwa da mutane tare da ceto mutum biyun da aka sace a Karamar Hukumar Toungo da ke Jihar jiya Lahadi.
Kakakin rundunar a Jihar, Suleiman Nguroje ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa yau Litinin.
Ya ce hakan na cikin irin nasarorin da suke samu a kokarinsu na yaki da satar mutane da fashi da makami da satar shanu da kuma rike makamai ba bisa ka’ida ba.
Suleiman ya kuma ce jami’an nasu sun sami nasarar kubutar da mutum biyun da aka sace daga hannun masu garkuwar, wadanda dukkansu mazauna kauyen Mayo Sasum ne da ke Karamar Hukumar ta Tounga.