An Karrama wasu Masu Yiwa Ƙasa Hidima A Gombe

0 396

Hukumar yiwa kasa hidima reshen jihar Gombe ta bada lambar yabo ga masu yiwa kasa hidima a jihar 12 daga cikin 1045 da suka samu horo na 2018 rukunin B kashin farko.

Jami’an hukumar a jihar Mr. David Markosn ya bayyana hakan yayin bikin yayesu a jiya Alhamis.

Ya ce wannan lambar yabo da aka bawa masu yiwa kasa hidimar ya biyo bayan managartan ayyukan koyarwa da suka gudanar a makarantun firamren yankin.

Mr. David ya ce an bada takardar girmamawa ga maza masu yiwa kasa hidima, yayin da aka bawa mata masu yiwa kasa hidima lambar yabo ta matan da suka yi fice.

Leave a Reply

%d bloggers like this: