An kama wata mata da ta kashe yayan kishiyarta 3 ta hanyar sanya guba a shayi
Rundunar Yan Sandan Jihar Yobe, ta kama wata Mata yar shekara 22 Mai Suna Khadija Yakubu, bisa zarginta da kashe Yayan Kishiyar ta 3 a yankin Malaria Huta ta karamar hukumar Patiskum ta Jihar.
Kakakin Rundunar ASP Dungus Abdulkareem shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Juma’a, inda ya ce Matar ta sanya Guba a Shayin Yayan Kishinyar ta su 4.
Yaran sune Umar Haruna, 12; Maryam Haruna, 11; Ahmed Haruna, nine and seven-year-old Zainab Haruna.
A cewarsa, bayan faruwar lamarin ne aka garzaya dasu zuwa Asibiti, inda aka tabbatar da mutuwar Yara 3, yayin da kuma akayi nasarar ceto Yaro 1 da ransa.
Kakakin Rundunar ya ce an kama Matar, inda ake cigaba da zurfafa bincike kan gaskiyar mutuwar tasu.