An kama wasu sabbin mutane 13 bisa zargin wawashe dukiyar jama’a a yayin zanga-zanga

0 182

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta sanar da kama wasu sabbin mutane 13 da ake zargi da hannu wajen wawashe dukiyar jama’a a yayin zanga-zangar.

Daga cikin kayayyakin da aka kwato sun hada da bale guda 316 na gidan sauro, buhunan taki 114, babur 1, naurar hasken rana guda 7, buhunan (zobo) 61/2, buhunan masarar guda 2, kujerun ofis 19, kujerun filastik 9. 

fanka 2, firiji 2, ƙofofi 4, Drawer ƙarfe 10, na’urar kashe wuta 2,  naurar CPU 2, da Stabilizer.

An kama tare da mayar da su a wuraren da aka dauka a kananan hukumomin Gumel, Roni da kuma B/Kudu. 

Sannan  an gurfanar da mutane 277 da ake tuhuma gaba daya.

Ya zuwa yanzu dai jihar Jigawa tana cikin kwanciyar hankali; babu wata zanga-zanga, barnatar da dukiya, ko asarar rayuka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: