Hukumar bayarda tsaro ga farin kaya ta Najeriya reshen jihar Katsina, ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da laifin fasa kwaurin wutar lantarki a jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar , Buhari Hamisu, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da wadanda ake zargin a Katsina a jiya Juma’a, ya ce an samu nasarar ne bisa hadin gwiwar da al’umma suka baiwa hukumar.
A cewarsa, rundunar ta samu nasarar cafke mutanen biyu, Aminu Sani, mai shekaru 19 da Ahmed Abdullahi, mai shekaru 23, sakamakon hadin gwiwa da suka yi. Ya ce daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Sani na cikin wata tawagar wata kungiyar asiri ce da ta kware wajen lalata ababen more rayuwa da satar kayan gwamnati.