An kama wasu ma’aikatan lafiya da karkatar da katan 109 na gidan sauro a jihar Gombe

0 268

Ma’aikatar Lafiyar Jihar Gombe, ta sanar da kama Ma’aikata 7 wanda suke aiki a hukumar Lafiya a Matakin Farko ta Jihar reshen Kanana hukumomin Kwami da kuma Billiri, bisa zargin su da karkatar da Katan 109 na gidan Sauro wanda za’a raba a Jihar.

Da yake Jawabi ga manema Labarai, Kwamishinan Ma’aikatar Lafiya na Jihar Dr Habu Dahiru, ya ce kimanin Katan 100 na gidan Sauro daga karamar hukumar Kwami ne suka bata, kuma tuni suka kama mutane 4 bisa zargin su da hannu a karkatar da kayan.

Kwamishinan ya ce sauran Katan 9 na gidan Sauron sun bata ne a karamar hukumar Billiri kuma tuni suka kama Ma’aikata Lafiya 3 bisa zargin su da hannu a batan kayan.

Dr Dahiru, ya ce daga bayanan sirrin da suke samu ya yi nuni da cewa an kama motocin da suka yi safarar gidan Sauron zuwa wasu wurare na daban.

Kazalika, ya ce yawan Adadin gidan Sauran ya kai dubu 5,450 wanda aka karkatar da su.

Kwamishinan ya ce matukar aka kama mutanen da laifin, za’a hukunta su kamar yadda kundin hukunta Ma’aikatan Gwamnati ya tanadar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: