An kama wasu abubuwan fashewa da makamai da alburusai a jihar Ribas

0 252

Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ta kama wasu abubuwan fashewa da makamai da alburusai daga hannun ‘yan kungiyar asiri a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Grace Iringe-Koko, ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata a Fatakwal.

Ta ce rundunar ‘yan sanda da ‘yan banga na cikin gida sun kama wani da ake zargin dan kungiyar asiri ne, mai suna Samuel Nwokoma, wanda ya kai su inda aka boye makaman a unguwar Diobu da ke Fatakwal.

Tace Kamen da akayi tare da kwace kayakin da aka kama ya zama wani gagarumin ci gaba wajen magance yawaitar hare-hare da kashe-kashen da ake samu na masu alaka da kungiyar asiri a Diobu. Iringe-Koko ta bayyana cewa, bayan yi masa tambayoyi ya amsa cewa yana da hannu a hare-hare biyu masu alaka da kungiyar asiri a yankin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: