An kama wani mutum mai shekaru 53, mai suna Usman Tela Ahmadu, wanda ke gudun hijira daga Maiduguri, a jihar Borno, da dan asalin karamar hukumar Yola ta Arewa, bisa laifin yin lalata da wata yarinya mai tabin hankali.
Kwamishinan ‘yan sanda (CP), Afolabi Babatola, ya nuna damuwarsa dangane da faruwar lamarin, ya kuma yi kira ga iyaye da su sanar da jami’an tsaro ayyukan bata gari domin daukar matakan da suka dace. CP Babatola, wanda ya bayyana cewa babu wata maboya ga masu aikata laifuka a jihar Adamawa, ya ce an tanadi dabarun binciken masu aikata laifuka a fadin jihar.