Wadanda ake zargi sun nuna wa jami’an tsaron gawar almajirin bayan sun fille masa kai kana suka sanya shi cikin buhu tare da binne shi a wani rami mara zurfi.
Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa a Nijeriya ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da kashe wani yaro Almajiri dan shekara 10 a karamar hukumar Jada da ke jihar.
A wata sanarwar da ta fitar a ranar Lahadi a shafinta na X da ke dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar SP. Suleiman Nguroje, rundunar ta ce ana zargin wani Ibrahim Abdul Malik mai shekara 27 da Aliyu Abdul Malik mai shekara 18, mazaunan Anguwar Sarkin Yamma a Jada, da kashe almajirin mai suna Abdalla Lawali ta hanyar fille masa kai.
Tun dai a ranar 7 ga watan Maris aka sanar da ɓacewar Abdallah. Bayan shafe kwanaki ana bincike da kuma nemansa ne, aka samu wasu bayanan sirri da suka taimaka wa jami’an ‘yan sanda gano inda waɗanda ake zargi suke.
Wadanda ake zargin sun nuna wa jami’an tsaron gawar almajirin da suka fille masa kai kana suka sanya shi cikin buhu tare da binne shi a wani rami mara zurfi.
Matasan biyu dai sun amsa laifinsu a yayin da suke amsa tambayoyi, inda suka ce sharrin shaiɗan ne, a cewar sanarwar ‘yan sandan.
Kwamishinan ‘yan sanda jihar Dankombo Morris ya yi Allah da mummunar aika-aikar kana ya ba da umarnin miƙa ƙarar zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na jiha (SCID) don gudanar da bincike mai zurfi da kuma ƙarin wasu tuhume-tuhume da hukunci.