An kama tare da kwace haramtattun kayayyaki a shiyyar Arewa da suka kai sama da ₦3Bn

0 187

Hukumar hana fasa kwabri ta Najeriya, sashin ayyuka na tarayya ta kama tare da kwace haramtattun kayayyaki a shiyyar Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya da suka kai sama da Naira biliyan uku.

Daga cikin kayayyakin da aka kama sun hada da katan-katan na tramadol 58, 750 da kuma ampulles na allurar analgin 48,000 da ake kai wa ‘yan bindiga a dajin Saminaka da ke karamar hukumar Lere a jihar Kaduna.

Da yake zantawa da manema labarai kwanturolan hukumar Bello ya bayyana cewa, jami’an hukumar ta Kwastam da ke aikin leken asiri, sun kama wata babbar mota dauke da buhu 750 na kasusuwan jakuna da nama.

Kwanturolan ya bayyana cewa an boye tramadol din a cikin motar dauke da kayan gyara motoci domin kaucewa idon jami’an kwastam da ke kan hanyar Saminaka/Kafanchan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: