Rundunar ‘yansandan Najeriya ta sanar da cewa ta kama mutum 751 da take zargi da aikata laifukan zamba ta intanet a 2024.
Kafar talabijin ta Channels ta ruwaito kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, yana bayyana alƙaluman, inda ya ce sun yi sa’ar hukuncin kotu da ya ɗaure 14 daga cikinsu.
Ya ƙara da cewa akwai lamurra 508 da suke ci gaba da aiki a kansu zuwa yanzu.
Adejobi ya kuma bayyana cewa sun ƙwato jimillar kuɗi dala 840, 000 na mutanen da aka damfara, yayin da aka riƙe jimillar naira miliyan N914 da wasu dala 115,000 a asusun bankuna daban-daban, ciki har da na crypto.
Haka nan, rundunar ta yi nasarar ƙwato ababen hawa 26, da gidaje 16, da filaye 39, in ji Mista Adejobi.