An kama mutum 12 bisa zargin kashe wani matashi a masallaci a jihar Kaduna

0 46

Rundunar ‘yansadan Najeriya reshen jihar Kaduna ta ce ta kama mutum 12 da zargin kai hari masallaci a Kaduna da ke arewacin ƙasar.

Wata sanarwa da kakakin rundunar a Kaduna, DSP Mansur Hassan, ya fitar ta ce harin ya yi sanadin kashe wani matashi mai suna Usman Mohammad mai shekara 23.

A cewar DSP Mansur, rundunar ‘yansandan ta samu rahoto daga wani mazaunin yankin Rigasa cewa ‘yandaba ɗauke da makamai na shirin kai hari kan masu sallar Tahajjud.

“Da jin rahoton ne kuma dakaru suka bazama amma kafin su ƙarasa har sun daɓa wa wani matashi mai suna Usman Mohammed wuƙa, wanda likita ya tabbatar da mutuwarsa a asibiti,” in ji shi.

Ya ce sun isa wurin ne bisa rakiyar dakarun sa-kai na Civilian Joint Task Force (CJTF), kuma tuni sun ƙaddamar da cikakken bincike kan lamarin.

Leave a Reply