An kama mutane takwas da ake zargi da hannu a kisan wani malami

0 195

Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta ce ta kama mutane takwas da ake zargi da hannu a kisan wani malami da ke koyarwa a sashen ilimin motsa jiki da ke jami’ar Maiduguri.

Kakakin rundunar ASP Daso Kenneth, ya shaida wa Manema labarai cewa waɗanda ake zargin an kama su ne bayan wani rahoto da babban jami’in tsaron jami’ar ya shigar.

A cewar kakakin, babban jami’in da ke gadin jami’ar ya kai rahoto ofishin ƴan sanda da safe cewa an ga wata gawa a ofishi wadda aka gano ta Dakta Abdulkadir Kamal ce.

Kakakin ya ƙara da cewa da samun rahoton, aka aike ƴan sanda zuwa wajen inda kuma aka kai gawar asibiti domin yin bincike a kanta. Ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano mutanen da ke da hannu a aika-aikar duk da cewa sun kama mutane takwas da ake zargi suna da hannu a kisan malamin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: