An kama mutane 54 bisa laifin karuwanci da ta’ammali da miyagun kwayoyi a Hadejia

0 1,077

Kwamatin tsaro na Karamar Hakumar Hadejia ya kama mutane 54 bisa laifin karuwanci da ta’ammali da miyagun kwayoyi da sauran laifuka.
Mutanen sun hada da mata 29 masu zaman kansu, 14 daga cikin su na dauke da cutar HIV, da Kuma Maza matasa 25.

Shugaban Karamar Hakumar Hadejia Alh Abdulkadir Umar Bala ya shawarce su da su koma gidajen iyayensu Neman neman yafiya da gafara.

Kwamatin tsaro wanda ya hada da dukkan jami’an tsaro ya iaddamar da sumamen da ya kai ga kamo mutanen a jiya lahdi a unguwar Gandun sarki.
Sana’ar karuwanci da Shan miyagun kwayoyi a jihar Jigawa ya saba doka da ka’ida.

Leave a Reply

%d bloggers like this: