An kama mutane 5 bisa zargin sata, da lalata dukiyoyin jama’a a jihar Jigawa

0 243

Rundunar yansandan jihar jigawa ta kama mutane 5 bisa zargin sata, da lalata dukiyoyin jama’a dana gwamnati da kuma dillacin miyagun kwayoyi.

A cewar kakakin hakumar DSP Lawan Shiisu Adam wanda ya tabbatar da hakan, yace sun gano kayayyaki da suka hada bindiga kirar gida, barudu, wuka, miyagun kwayoyi kayan abinci, da wayoyin lantarki da sauran kayayyaki da ake zargin na sata ne.

Yace sun kama mutanen ne yayin wani sumame da suka kaddamar a karamar hakumar Roni. kakakin yace yayin bincike, wadanda ake zargin amsa laifin na mallakar wayopyin lantarki na sata daga gidan shugaban karamar hakumar Roni.

Leave a Reply

%d bloggers like this: