An kama mutane 13 kan zargin fashi da makami da satar kayan abinci a jihar Ribas

0 146

Rundunar ‘yansanda reshen jihar Ribas ta kama mutane 13 da zargin fashi da makami, da satar kayan abinci.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ta fitar ta ce cikin waɗanda ake zargin akwai soja huɗu, da ɗan rundunar tsaro ta Civil Defence.

Grace Iringe-Koko ta ce sun yi nasarar kama mutanen ne sakamakon wani “bincike na tsanaki” bayan kama wani da ake zargi da haura gidan ajiyar abinci a ƙaramar hukumar Ohio/Akpor ta jihar.

Tace biyu daga cikin mutanen farko da aka kama kofur-kofur ne a rundunar sojin Najeriya da ke aiki a jihar Delta, da kuma jami’i a rundunar tsaro ta Civil Defence mai aiki a Kabba da ke jihar Kogi.

Ta ƙara da cewa daga baya ne suka gano wani babban gungu na masu aikata fashi da kuma karkatar da kayan mutane, ciki har da manyan motoci. 

A cewarta, rundunar ta ƙwace mota ƙirar Toyota Hilux da gungun mutanen ke amfani da ita.

Leave a Reply

%d bloggers like this: