An kama masu zanga-zanga 1,133 a Turkiyya cikin kwana biyar

0 34

An kama masu zanga-zanga sama da 1,100 tare da tsare su saboda gudanar da zanga-zangar nuna adawa da kama Magajin Garin Istanbul, Ekrem Imamoglu.

An kama Imamoglu ne a ranar Laraba ta makon jiya, inda gwamnatin ke tuhumarsa da cin hanci da taimakon ƙungiyar ta’addanci.

Haka kuma an tsare masu zanga-zangar sama da 70 a Kocaeli da ke kusa da Istanbul.

Haka kuma ƴansanda sun kama wasu ƴansiyasa da lauyoyi da aƙalla ƴanjarida guda goma a wani samame da suka kai a birnin Izmir da ke Istanbul.

Leave a Reply