An kama masu sayarda magunguna ba bisa ka’ida ba guda 350 a jihar Jigawa

0 237

Hukumar da ke kula da harhada magunguna ta Najeriya ta kama, tare da gurfanar da wasu masu sayarda magunguna ba bisa ka’ida ba tare kuma da rufe shagunan sayar da magunguna 350 a jihar Jigawa.

Daraktan hukumar Pharmacist Stephen Esumobi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan ayyukan hukumar a sakatariyar gwamnatin tarayya dake Dutse, babban birnin jihar Jigawa.

Stephen Esumobi ya bayyana cewa an rufe jimillar guraren sayarda magani 355 da suka hada da manyan shagunan sayarda magani 8, da kananan shagunan sayar da magunguna 87, da kuma wasu Karin shagunan sayar da magunguna 260 da aka samar ba bisa ka’ida ba.

Ya ce an yi hakan ne domin tabbatar da cewa dukkan magungunan sun kasance masu inganci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: