An kama kwalaben Kodin fiye da 1,200,000 a Najeriya

0 215

Jami’an hukumar Hana sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta najeriya sun kama kwalaben kodin miliyan 1,229,400 a cikin wasu kwatenoni bakwai a tashar jiragen ruwa ta Onne da ke birnin Fatakwal.

Cikin wata sanarwa da kakakin hukumar Femi Babafemi ya fitar, ya ce an yi ƙiyasin kuɗin kodin din ya kai fiye da naira biliyan 9.8.

Kamen na zuwa ne ƙasa da mako uku da jami’an hukumar suka kama wasu kwalaben kodin fiye da miliyan guda a birnin na Fatakwal.

Kamen na daga cikin jerin samamen da jami’an hukumar ke ƙaddamarwa kan tasoshin ruwan ƙasar, da nufin kakkaɓe safarar ƙwaya a tasoshin ruwan ƙasar.

Hukumar ta ce bincikenta ya gano cewa an shigar da ƙwalaben daga ƙasar Indiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: