An kama kimanin mutane 13 bisa zargin su da kisan fiye da mutum 20 a jihar Filato

0 272

Rundunar Yan Sanda ta kama Kimanin mutane 13 bisa zargin su da kisan da akayi cikin karshen Makon da ya gabata.

Kakakin Rundunar Yan Sanda ta Kasa Frank Mba, shine ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa a jiya Litinin, inda ya ce kimanin mutane 33 aka kama bisa zargin su aikata laifukan.

A cewarsa, DIG Sanusi Lemu, shine zai kasance mai Jagorantar  binciken, kuma tuni sukayi hadin gwiwa da rundunar da take jihar Plateau domin yin bincike tare da kwantar da hankali a wuraren.

Haka kuma ya kara da cewa IGP Usman Baba Alkali, ya bada umarnin sake tura karin Jami’an tsaro domin samar da zaman lafiya a yankin Rukubu da wasu yankunan.

Kazalika, ya ce an tura Jirgin mai saukar Ungulu domin tabbatar da cewa ba’a sake samun barazanar tsaro a wuraren da lamarin ya faru ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: