An Kai Tallafi Ga Mutanen Da Ambaliyar Ruwa Ta Yiwa Ɓarna

0 363

Hukumar kula da lafiyar jiragen ruwa ta kasa ta raba kayan Tallafi na milyoyin naira ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a yankin jihar Katsina.

Da ya ke meka kayayyakin ga Gwamnatin jihar ta Katsina daraktan hukumar Alhaji Ibrahim Jibril ya ce manufar wannan rabo shi ne domin saukakawa wadanda ambaliyar ta raba da muhallansu.Ya ce hukumar tana amfani da Gwamnatin domin tallafawa wadanda suka gamu da wani iftila’i.

Kazalika ya kara da cewa wannan Tallafi zai karawa gwamnati kaimi wajen kyautata zamantakewar al’ummar kasar nan.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa kayayyakin da aka raba sun hada da shinkafa, sikari, gero, mai da kuma sabulun wanka dana wanki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: