An kaddamar da rabon tallafin rage radadi ga magidanta 15,775 a jihar Jigawa

0 133

Gwamnan jihar Jigawa, Mallam Umar A. Namadi FCA ya ƙaddamar da rabon tallafin rage raɗaɗi ga waɗanda ibtila’in ambaliyar ruwa ta ritsa da su da ke zaune sa sansanonin yan ambaliyar ruwa guda 12 da ke jihar nan. Kimanin magidanta 15,775 za su amfana da wannan tallafi.

Kowane magidanci zai amfana da buhun gero mai nauyin 10kg, masara mai nauyin 10kg, shinkafa mai nauyin 10kg, kwalin taliya da kuma kuɗi N20,000.

An ƙaddamar da wannan tallafi a ƙaramar hukumar kiyawa, wadda aka raba wa mutane kimanin 3,222 sai kuma ƙaramar hukumar Buji da aka raba wa mutane 1,200. Ƙananan hukumomin Kiyawa da Buji suna cikin ƙananan hukumomi kimanin 20 da aka samu matsalar ambaliyar ruwa a jihar Jigawa.

Bayan wannan ƙaddamarwa, hukumar agajin gaggawa ta jiha za ta ci gaba da raba wannan tallafi a sauran ƙananan hukumomin da ke da matsugunnan ‘yan ambaliyar ruwa (IDPs).

Ambaliyar ruwan sama da aka samu a jihar Jigawa, ta shafi sama da mutane 50,000, ta janyo asarar rayuka kimanin 33, ta ruguza gidaje sama da 7,000 da gonakai kusan 10,000.

A cikin jawabinsa, gwamna Namadi ya sake miƙa saƙon jaje ga waɗanda ibtila’in ambaliyar ruwan ta shafa, ya kuma shaida musu da cewar; wannan tallafi da aka raba musu ba zai iya dawo musu da abin da suka rasa ba, sai dai ya rage musu raɗaɗin halin da su ka tsinci kasuwansu.

Daga ƙarshe gwamnan ya jaddada godiyarsa ga gwamnatin tarayya, ƙarƙashin shugabancin shugaban ƙasa sanata Bola Ahmed Tinubu bisa irin tallafin da gwamnatin tarayya ya bayar, ya yabawa ɗankasuwa Alhaji Ɗahiru Mangal, da tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma ministan tsaron Najeriya, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, bakunan UBA da JAIZ da sauran dukkan waɗanda suka bayar da gudunmawa ga waɗanda ambaliyar ta shafa. Ya kuma hori ‘yan kwamatin rabon kayan da su ji tsoron Allah wajen wannan rabo, su tabbatar kayan ya je hannun waɗanda abin ya shafa kai tsaye.

Leave a Reply

%d bloggers like this: