An kaddamar da rabon kayan amfanin gona a karkashin shirin NG-CARES Fadama kashi na uku

0 287

Gwamna Mallam Umar Namadi ya halarci bikin kaddamar da rabon kayan amfanin gona ga kungiyoyin manoma a karkashin shirin NG-CARES Fadama kashi na uku.

A cikin jawabinsa, gwamnan ya yaba da tsarin zabar wadanda suka ci gajiyar shirin cikin gaskiya da adalci.

Shirin ya kunshi mutane dubu4 da 220 daga sassa daban-daban na jihar Jigawa don mayar da hankali wajen samar da amfanin gona da kuma samar da abinci.

Magidanta masu karamin karfi dubu  10 da dari 730 ne suka ci gajiyar shirin tun farko. Gwamnan ya bayyana cewa sabon tsarin da Bankin Duniya ya samar zai yi amfani da karin masu cin gajiyar shirin mutun  dubu 30.

Leave a Reply

%d bloggers like this: