Asusun Tallafawa wadanda rikicin ya shafa tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Yobe, ya kaddamar da gine-gine tare da gyare-gyaren wasu cibiyoyin koyon sana’o’i a yankunan jihar Yobe guda tara domin dawo da wadanda rikicin Boko Haram ya shafa.
Shugaban asusun, Janar Theophanous Danjuma wanda babban darakta, Farfesa Nana Tanko ya wakilta, ya bayyana cewa za a yi amfani da kimanin naira miliyan 130 don gyarawa tare da samar da kayan aikin kwamfutoci da injinan man gyada da wuraren sarrafa su da dai sauransu.
Kwamishinan kula da ayyukan jin kai a jihar wanda Daraktan Agaji Kaku Jawi ya wakilta, ya yabawa kungiyar bisa yadda ta shiga tsakani a yankuna 9 rikicin Boko Haram ya shafa jihar Yobe.