An harbe wani dan gungun ‘yan fashin daji da ke addabar mazauna jihar Kaduna

0 216

An harbe wani dan gungun ‘yan fashin daji da ke addabar mazauna jihar Kaduna.

An rawaito cewa an kashe dan fashin ne yayin musayar wuta da jami’an tsaro a kusa da kauyen Kasarami da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

A cewar wata majiya daga yankin, lamarin ya faru ne da sanyin safiyar yau.

Wani shugaban matasa, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce an kashe fararen hula biyu yayin da ‘yan bindigar suka lalata motar jami’an tsaro yayin musayar wutar.

Shugaban matasan ya ce an kashe direba da kwandasta da ke tafiya a lokacin da lamarin ya faru.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Jalige Mohammed, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce jami’an tsaro sun dakile harin kuma an kashe wani dan bindiga yayin da matafiya biyu suka mutu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: