An hana ma’aikatan asibiti mining a jihar Gombe

0 149

Hukumar gudanarwar asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya da ke Gombe wato Federal Teaching Hospital ya fitar da wata sanarwar hana dukkannin wani abu mai kama da mining da zai ɗauke hankalin ma’aikaci daga kula da mara lafiya.

Sanarwar dai wadda mataimakin darektan gudanarwa na asibitin ya sanya wa hannu ta ce:

“An umarce shi da ya gargaɗi ma’aikata su guji yin mining ko kuma duk wata hanyar neman kuɗin kirifto a lokacin da suke bakin aiki…”

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa ” za a ɗauki tsattsauran mataki ga duk ma’aikacin da aka samu yana karya wannan umarni.”

Sanarwar ta bayyana cewa “an ɗauki matakin ne sakamakon irin ƙorafe-ƙorafen da hukumar asibitin ke samu daga marasa lafiya da danginsu da ke nuna irin yadda mining ɗin da ma’aikatan ke yi yake ɗauke hankalinsu daga kula da marasa lafiya.”

A lokacin da ake zanatawa da ma’aikatan, ra’ayoyin su banbanta inda wasu suka amince da hukuncin cewa ya kamata, yayin da wasu kuma suke ganin kamar ya yi tsauri.

Leave a Reply

%d bloggers like this: