An hana gudanar da wasa ko tseren dawaki yayin bukukuwan Sallah a Minna

0 280

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta hana gudanar da wasa ko tseren dawaki a Minna, babban birnin jihar a yayin bukukuwan Sallah.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Shawulu Ebenezer Dan-mamman, wanda ya bayyana hakan a cikin wani sakon barka da Sallah mai dauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar, Wasiu Abiodun, ya ce an hana wasa da dawaki a jihar domin hana bata gari kai hari a lokutan bukukuwa da suka saba yi.

Abiodun ya ce kimanin jami’an su 2,500 ne aka tura domin samar da tsaro a dukkan filayen idi na kananan hukumomi 25 na jihar, da wuraren shakatawa da sauran wuraren taruwar jama’a. Hakazalika Gwamnan Jihar ta Neja Mohammed Umaru Bago ya bukaci al’ummar Musulmi da su yi amfani da lokacin Sallar Idi domin yin addu’o’in zaman lafiya da tsaro a Jihar da ma kasa baki daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: