An GwanGwaje Alhazan Garin Auyo Na Jigawa

0 329

Shugaban Karamar Hukumar Auyo, Alhaji Umar Musa Kalgwai, ya bayar da kyautar Riyal 50, kimanin Naira 4,812 ga dukkan maniyyata 26 da suka fito daga yankin Karamar Hukumar.

Musa Kalgwai ya bayyana hakan a Auyo yayinda yake bankwana da maniyyatan, inda ya shawarcesu to suke kula da jakunkunansu saboda aikin masu safarar kwayo dake labe a kowane filin jiragen sama a kasar.

Daga nan sai ya hore su da suyi addu’ar neman zaman lafiya da cigaban Najeriya, kuma sai ya gargadesu da su kauracewa aikata abubuwan da su zubarwa da kasar mutunci a idon duniya.

Da yake mayar da jawabi a madadin maniyyatan, Alhaji Muhammad Anauya, ya godewa karamar hukumar bisa tallafin inda yayi alkawarin cewa maniyyatan zasu zamo jakadu nagari ga kasar a kasa mai tsarki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: