An gudanar da taron buda baki na azumin Ramadan tare da Almajirai a jihar Kano

0 224

Mambobin majalisar kula da kananan yara ta jihar Kano, sun gudanar da taron buda baki na azumin Ramadan tare da Almajirai a jihar.

Da take jawabi yayin taron buda bakin Rt. Hon. Hauwa Muhammad Ibrahim, “ta ce wannan wani bangare ne na tallafawa Almajirai da muke tare da su anan wadanda suka zo jihar da nufin neman ilmin addinin Muslunci.

Hauwa, ta kara da cewa wannan karamci zai kara kawo kusanci ga yara marasa galihu da kuma wadanda suke matukar bukatar a tallafa musu a  kowanne lokaci. Kazalika Hauwa, ta yi kira ga majalisar dokokin jihar Kano, da ta goyi bayan shirin na tallafawa marasa galihu a cikin al’umma kasancewar suna da matukar bukatar a taimaka musu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: