An gudanar da taron bayar da horo ga matan Fulani 60 kan sarrafa abinci mai gina jiki a jihar Jigawa

0 330

Ma’aikatar Jindadi walwalar jama’a ta jihar Jigawa ta gudanar da taron bayar da horo ga matan Fulani 60 dake kauyen Gafaya dake Karamar hakumar Kafin hausa kan sarrafa abinci mai gina jiki.
Kwamishiniyar ma’aikatar Hajia Hadiza T. Abdulwahab ce ta bayyana hakan a lokacin rabon tallafin naira dubu 600 ga mata 60.
Ta nanata kudirin gwamna Malam Umar Namadi na shigar da mata cikin shirin samar da abinchi mai gina jiki ga mata masu juna biyu da kuma kananan yara.
Hajia Hadiza ta kara da cewar an bada horan ne ga matan Fulani domin nuna musu hanyoyin sarrafa abincin gida mai gina jiki domin amfanin mata masu ciki da kananan yara.
Ta bada tabbacin gwamnatin jiha na dawo da shirin haihuwa lafiya tare da hadin gwiwar kungiyar direbobi domin samun saukin kaiwa mata masu ciki asibiti a lokacin haihuwa.
A jawabinta Daraktar harkokin mata Hajia Adama Umar Zandam ta yaba da halartar matan wajen taron tare da fatan zasu yi amfani da ilmin da suka koya.
A sakon ta na fatan alheri sakatariyar zartarwa ta hukumar kula da makarantun ya’yan Fulani makiyaya ta jiha ta hannun Hajia Ramatu Umar Saleh ta yaba da shigo da matan Fulani cikin shirin haihuwa lafiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: