Kwamatin gwamnatin jihar jigawa na man fetur ya gargadi gidajen mayuka dangane da matse litar man fetur da kuma karin farashi ba bisa ka’ida ba.
Shugaban kwamatin Kanal Muhammad Alhassan mai ritaya yayi wannan gargadi yayin ziyarar sanya ido a wasu gidajen mayuka da ke birnin Dutse.
Yace kwamatin ya gano yadda wasu gidajen mayukan da suke algus da kuma kara farashi ba bisa ka’ida ba. Alhassan yace kwamatin zai dauki tsauraran matakai domin ladabtar da masu gurbata litar mai.