An gabatar da ƙudirin da zai yiwa dokar masarautar sarkin Musulmi kwaskwarima

0 201

An gabatar da kudirin dokar yin gyara ga sashe na 76, kashi na biyu na dokar ƙananan hukumomin jihar Sokoto a gaban majalisar dokokin jihar a yau Talata.

Ƙudurin dai ya janyo ce-ce-kui-ce, kasancewar ana ganin idan aka amince da dokar za ta rage ƙarfin iko na mai alfarma sarkin Musulmin Najeriya, Sa’ad Abubakar III.

Bayan gabatar da ƙudurin a zauren majalisar, nan take aka yi masa karatu na farko da na biyu, sannan aka miƙa shi ga kwamitin da ke lura da ƙananan hukumomi da masarautu.

An bai wa kwamitin kwana 10 domin tattaunwa tare da gabatar da rahoto a zauren Majalisar.

Idan aka amince da dokar, za ta soke gyaran da aka yi na shekara ta 2008, wadda ta bai wa sarkin Musulmi damar naɗa hakimai da iyayen ƙasa kai tsaye.

Hakan na nufin sarkin Musulmin ba zai iya naɗa irin waɗannan muƙamai ba har sai ya samu sahhalewar gwamnan jihar, kamar yadda ake yi gabanin shekarar ta 2008.

A kwanakin baya ne gwamnan jihar, Ahmad Aliyu ya sauke wasu daga cikin hakiman da masu riƙe da masarautun gargajiya da ke jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: