Al’ummar garin Wanzamai dake karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara sun fitar da jerin sunayen mutane 85 da ake zargin ‘yan ta’adda sun sace a ranar Juma’a.
Duk da cewa cikin jerin sunayen ba a bayyana shekarun wadanda abin ya shafa ba, majiyoyi sun ce wadanda abin ya shafa sun hada da mata da kananan yara.
Da take magana da Sashen Hausa na BBC kan harin, wata uwa da ta ce an sace ‘yar ta mai shekaru 15, ta bayyana damuwarta kan halin da yaran da ake garkuwa da su ke ciki.
Kamar yadda wani mahaifi ya bayyana cewa lamarin ya shafi duk wani gida da ke cikin yankin.
A halin da ake ciki, yunkurin da manema labarai suka yi na jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara bai yi nasara ba, domin lambar wayarsa da aka sani bata shiga har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Har ila yau, Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Zamfara, Mamman Tsafe, bai dauki waya ko amsa sakon da manema labarai suka aika zuwa layinsa ba.
- Comments
- Facebook Comments