An fara bincike kan zargin karkatar da kudaden tallafin annobar korona

0 215

Kwamitin Majalisar Wakilai na kasa, ya kaddamar da fara cikakken bincike kan zargin karkatar da kudaden tallafi na annobar COVID-19 daga ma’aikatu, da sassan hukumomin gwamnati.

Wani dan majalisar wakilai, Nyampa Zakari, a watan Oktoba, ya gabatar da kudirin binciken, yana zargin ma’aikatun da karkatar da kudaden da ya kai Naira bilyan 183 da mliyan dari 9 da aka ware domin magance cutar ta COVID-19 daga 2020 zuwa 2023.

A jawabin bude taron, shugaban kwamitin, Bamidele Salam, ya gargadi hukumomin da abin ya shafa cewa kwamitin ba zai saurari koke-koke na karin lokaci ba.

Dan majalisar ya bukaci ofishin Akanta Janar na tarayya da ya samar da ma’aikatan da suka dace da kuma kwararrun da za su taimaka wa kwamitin wajen gudanar da ayyukansa.

Wasu daga cikin hukumomin da suka bayyana gaban kwamitin a jiya Litinin sun hada da. Asibitocin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi, da ma’aikatar sadarwa ta tarayya, cigaban da tattalin arziki na zamani, da ma’aikatar noma da samar da abinci ta tarayya, da ma’aikatar albarkatun ruwa ta tarayya, da kuma hukumar kula da titunan gwamnatin tarayya da dai sauransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: