An Duƙufa Wajen Nemowa Ƴan Mata Da Almajirai Mafita
Wata kungiya mai suna Crowd Funding Initiative Mafita, mai aiki a jihohin Kaduna da Kano da Katsina da kuma Jigawa, ta shirya taron bita kan inganta rayuwar ‘yanmata da almajirai a Dutse.
A jawabinsa wajen bude taron bitar mukaddashin gwamnan jiha, Alhaji Umar Namadi, ya yabawa kungiyar bisa hangen nesanta wajen shirya taron bitar bisa muhimmancinta ga mahalarta da kuma jihohin huɗu.
Yace gwamnatin jiha zata bayar da duk wata gudunmawa data dace domin samun nasarar taron bitar, inda kuma ya bukaci mahalarta taron dasu tattaunawa a junansu tare da yin amfani da abubuwan da suka koya, a jihohinsu.
A jawabinsa na maraba, jagoran shirya taron bita,r Mallam Umar Muhammad yace sun shirya taronne domin lalubo hanyoyin dogaro da kai da za’a samawa ‘yanmata da almajirai, inda za a basu horo na koyan sana’o’in dogaro da kai.