An dawo lodin man fetur a depo-depo na Abuja da Legas

0 188

Akwai yiwuwar kawo karshen dogayen layuka a gidajen mai a wannan makon a wasu sassan kasarnan, yayin da aka dawo lodin man a depo-depo na Abuja da Legas.

An rawaito cewa  a ranar Asabat mamallakan depo-depo din sun rufe saboda zanga-zangar yunwa da aka fara a ranar Alhamis.

Direbobi da mamallakan manyan motocin daukar man sun kasance cikin barazana yiwuwar samun hare-hare yayin jigilar man.

Yankasuwar man a jiya Litinin, sun yi bayanin cewa zanga-zangar da ake cigaba da yi ce ta janyo tsayawar jigilar man da guarben da ake dora man. Jihohi da dama a kasarnan har da Birnin tarayya Abuja sun fuskanci fama da dogayen layuka a gidaje mai, abin da kamfanin main a kasa NNPCL, ya dora alhakin hakan kan tangarda da aka samu a hanyar fitar da man.

Leave a Reply

%d bloggers like this: