An damƙe wasu yan bindiga da ake zarginsu da kashe wasu masu ibada 18 a ƙaramar hukumar Mashegu dake jihar Niger
An damke wasu yan bindiga, da ake zarginsu da kashe wasu masu ibada 18 a garin Maza-Kuka dake karamar hukumar Mashegu dake jihar Niger.
Kwamshinan kananan Hukumomi na jihar da kuma ayyukan cikin gida Emmanuel Umar, shine ya bayyana hakan, a lokacin dayake zantawa da manema labarai a jiya laraba a birnin Minna.
Anasa bangaren kwamishinan yansanda na jihar DSP Wasiu Abiodun, bai bayyana adadin wadanda ake zargin ba, amma ya tabbatar da samun nasarar kamen.
Kwamishinan ya kara da cewa sun samu nasarar kama wasu mutane 6 da ake zargin su da kai harin da aka kashe mutane da dama a ranar 26 ga watan Oktoba na wannan na shekarar.
Inda ya bayyana sunayen su kamar haka, Mohammed lawali, Suleiman Ibrahim, Mohammed Rebo, Bashir Audu, Monsoru Abubakar and Abubakar Hamidu.